Ba zan koma jam’iyyar APC ba — Makinde
[ad_1]
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya musanta jita-jitarr shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Ya ce har yanzu yana nan daram a PDP duk da ficewar wasu gwamnoni zuwa jam’iyya mai mulki.
Makinde, ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da wani littafi da tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, ya rubuta.
Ya ce yawancin matsalolin Najeriya suna fitowa ne daga muradun ’yan siyasa masu ruwa da tsaki, ba daga talakawan ƙasar ba.
“Ni ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, kuma ba zan koma APC ba,” in ji Makinde.
Gwamnan, ya bayyana cewa yawancin ’yan Najeriya na son zaman lafiya da haɗin kai, amma ’yan siyasa na amfani da addini, ƙabilanci da yanki wajen rarraba kawunan mutane domin cimma muradunsu.
Ya kuma yi gargaɗi kan salon siyasar haddasa rarrabuwar kawuna da haɗin kan ƙasa.
A cewarsa, dole ne shugabanni su haɗa kai duk da bambancin jam’iyya domin inganta shugabanci da ci gaban ƙasa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link