Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru
[ad_1]
Rahotonni sun bayyana ɓarkewar zanga-zanga a birnin Douala, cibiyar kasuwancin Kamaru jim kadan bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.
Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a dandalan sada zumunta sun nuna gomman mutane sun fantsama kan titunan birnin, tare da rera waƙoƙin goyon bayan Issa Tchiroma Bakary, jagoran adawar ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran Kamaru, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin majalisar birnin, bayan da masu zanga-zangar suka far masa.
BBC ya ruwaito cewa, a yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan abin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru, makarantu da shaguna sun kasance a rufe a Yaoundé, babban birnin ƙasar.
Hatta ma’aikatan gwamnati da dama sun ƙi fita wuraren ayyukansu saboda fargabar abin da ka iya biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa girke jami’an tsaro masu yawa a manyan birane, musamman Yaoundé, Douala da kuma Garoua, mahaifar jagoran adawa Tchiroma Bakary, ya taƙaita zanga-zangar da aka fara gudanarwa.
Kawo yanzu, yawancin ‘yan ƙasar sun ci gaba da kasancewa a cikin gidajensu bayan da aka bayyana Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda hakan ke tabbatar masa da wa’adin mulki na takwas.
Shugaba Paul Biya shi aka sanar a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa karo na takwas a cewar Kotun Tsarin Mulkin Kamaru, yayin da tun farko jagoran ’yan adawa Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link