Adadin Mayaƙan ISWAP Da Aka Kashe A Borno Ya Kai 75
[ad_1]
Adadin mayaƙan ISWAP da aka kashe yayin wani hari a Jihar Borno ya ƙaru zuwa 75.
‘Yan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari kan sojojin Nijeriya a Malam Fatori, ƙaramar hukumar Abadam, da safiyar ranar Laraba, amma sojojin sun daƙile harin.
- Rawar Da Sashen Ayyukan Hidimomi Da Biyan Bukatu Ke Kara Takawa A Kasar Sin
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 29
Da farko an ce an kashe mutum 61, amma daga baya an tabbatar da cewa aƙalla mayaƙa 75 aka kashe, yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka.
Sojojin tare da haɗin gwiwar rundunar sojin saman Nijeriya sun gano harin da wuri tare da mayar da martani cikin gaggawa.
An kuma kai hare-hare ta sama kan waɗanda suka gudu, wanda ya ƙara jawo musu asara.
Haka kuma, rundunar sojin saman Jamhuriyar Nijar ta taimaka wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’addan da ke tserewa.
Jami’an tsaro sun kuma ƙwato makamai da alburusai da dama daga wajen, wanda ya ƙara rage ƙarfin ƙungiyar a yankin.
A ɓangaren sojoji, an jikkata sojoji huɗu amma ana kula da su kuma suna cikin ƙoshin lafiya.
[ad_2]
Source link