An ɗaure dillalin miyagun ƙwayoyi shekara 15 a Kano

[ad_1]



An yanke wa Jonathan Nuhu, mai shekara 45 da ke ƙauyen Kanke da ke Jihar Filato, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 15 sakamakon samunsa da laifin mallakar tabar wiwi.

Wannan hukunci zai fara aiki ne tun daga ranar da aka yanke shari’ar.

Kakakin Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a MN Yunusa, ne ya yanke hukuncin a ranar 17 ga Maris, 2026.

Ya bayyana cewa, jami’an NDLEA sun kama Nuhu ne a ranar 20 ga Yuli, 2023, kusa da gadar Wudil da ke ƙaramar hukumar Wudil a Jihar Kano, biyo bayan cafke buhunan tabar wiwi guda 116.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “An gaggauta gurfanar da shi gaban kotu. Bayan shafe shekaru uku ana bincike da shari’a, kotun ta same shi da laifin tare da yanke masa hukuncin zaman gidan yari.”

Maigatari ya ƙara da cewa, akwai bayanan da ke nuna cewa a baya ma Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Jigawa ta taɓa yanke wa Nuhu hukuncin shekaru 15 a gidan yari ranar 22 ga watan Yuni, 2021, kan makamancin wannan laifi.

A lokacin da aka kama shi da sabon laifin a Kano, yana waje ne a kan belin da aka ba shi yayin da yake jiran sakamakon ɗaukaka ƙara kan shari’arsa ta farko, lamarin da ya kai ga sake yanke masa wannan sabon hukuncin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *