Duk Wani Yunkuri Na Kawo Cikas Ga Dunkulewar Sin Ba Zai Yi Nasara Ba
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullun. Kuma dangane da atisayen soja, wanda sojojin ’yantar da jama’ar kasar Sin suka yi, a kusa da tsibirin Taiwan a yau din, ya ce Sin ba za ta sauya aniyarta ta kare ikon mulkin kai, da tsaro, da cikakkun yankunan kasar ba, kuma duk wani yunkuri na kawo cikas ga hadewar Sin waje guda ba zai yi nasara ba.
Dangane da halin da ake ciki a kudancin Yemen kuwa, Lin Jian ya ce Sin ta mayar da hankali kan halin da ake ciki a kudancin kasar, kuma tana kira da a kiyaye ikon mulkin kan kasar Yemen, da hadin kan kasar, da kuma kare cikakkun yankunan kasar. Lin ya yi fatan dukkan bangarorin kasar za su sanya muradun al’ummun Yemen a gaban komai, da kuma raba baya ga kokarin da Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da sauran yankuna da kasashe, da kuma al’ummar duniya ke yi na samar da zaman lafiya.
Da yake amsa tambaya game da rikicin Ukraine, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin tana goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka, wajen samar da zaman lafiya, kuma za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Bugu da kari, game da sanarwar da Isra’ila ta fitar a kwanan nan, ta amincewa da ‘yancin kan yankin Somaliland, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan kare ikon mulkin kan kasar Somaliya, da ’yancin da kare cikakkun yankunan kasar, kuma tana adawa da duk wani mataki na raba yankunan Somaliya. (Safiyah Ma)