Sin Ta Amsa Tambayoyi Game Da Harin Soja Da Amurka Ta Kai Wa Venezuela
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayoyi game da harin soja da Amurka ta kai wa Venezuela jiya Asabar.
Kakakin ya ce, Sin ta yi matukar mamakin yadda Amurka ta yi amfani da karfi ba tare da kunya ba ga wata kasa mai cikakken iko, har ma ta kai ga afka wa shugaban kasar, Sin na matukar tir da hakan. Irin wannan babakere na Amurka ya saba wa dokokin kasa da kasa sosai, ya kuma keta ikon mulkin Venezuela, ya kuma yi barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin Latin Amurka da Caribbean, kuma Sin na adawa da shi sosai. Sin tana kalubalantar Amurka da ta bi dokokin kasa da kasa da kuma manufa da ka’idojin yarjejeniyar MDD, ta daina keta tsaron ikon mulki na wasu kasashe. Kazalika, Sin ta yi kira ga Amurka da ta tabbatar da kiyaye lafiyar shugaba Nicolas Maduro da uwargidansa, da sakinsu nan da nan ba tare da wani sharadi ba.
Da sassafe ranar 3 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta kaddamar da matakin soja a Venezuela, inda ta kai hari ba zato ba tsammani kan Caracasga, babban birnin kasar Venezuela, ta kuma yi awon gaba da shugaban kasar Nicolas Maduro da matarsa. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, Amurka za ta tafiyar da ragamar harkokin Venezuela har sai an samu canjin mulki yadda ya kamata. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link