AFCON 2025: Yadda Wasannin Zagayen ‘Yan 16 Za Su Kasance

[ad_1]

Daga Abba Ibrahim Wada

A ranar Talata Senegal ta doke Benin da ci 3-0 domin shiga zagaye na 16 na gasar AFCON ta bana a matsayin wacce ta kare a matsayi na daya a rukunin D, wanda hakan ya ba Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo damar zama ta biyu a rukunin, wanda hakan ke nufin za ta buga da Algeria a wasan zagaye na gaba na gasar.

Senegal wadda Sadio Mane ke jagoranta, wacce kuma ta lashe gasar ta kasashen Nahiyar Afirka a shekarar 2022, ta shiga zagaye na karshe na wasannin rukuni da fatan doke Benin a Tangier, tare da fatan kar abokan hamayyarta kasar Congo ta wuce su da bambancin kwallaye, Senegal ta yi nasara da ci 3-0 a kan Benin, inda Abdoulaye Seck da Habib Diallo suka zura kwallaye kafin a bai wa kyaftin din tawagar Kalidou Koulibaly katin kora bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Cherif Ndiaye ne ya zura wa Senegal kwallonta ta karshe a wasan.

A daya wasan kuma Jamhuriyar Congo ta doke Botswana da aka riga aka cire daga gasar da ci 3-0 a Rabat, hakan na nufin manyan kasashen biyu sun kammala wasan rukuni da maki bakwai daga wasanni uku, amma Senegal wadda Pape Thiaw ke jagoranta ta mamaye rukunin da bambancin kwallaye biyu, Senegal za ta ci gaba da kasancewa a birnin Tangier domin buga wasan zagaye na 16 a ranar Asabar da wadda ta kare a matsayi na uku a rukunin E.

Jerin Wasannin Zagayen 16 Na Gasar AFCON

Ranar Asabar, 3 Ga Watan Janairu

Senegal Da Na 3 A Rukunin E 4:00 (Tangiers). Mali Da Tunisia 7:00 (Casablanca)

Ranar Lahadi, 4 Ga Watan Janairu

Morocco Da Tanzania 4:00 (Rabat) Afirka ta Kudu Da Na 2 A Rukunin 7:00 (Rabat)

Ranar Litinin 5 Ga Watan Janairu 5

Masar Da Benin 4:00 (Fes). Nijeriya Da Na 3 A Rukunin 7:00 (Fes)

Ranar Talata 6 Ga Watan Janairu

Algeria Da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo 4:00 (Rabat) Kasa Ta 1 Da Kasa Ta 2 A Rukunin E 7:00 (Marakesh)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *