Binciken CGTN: Ya Kamata Hadin-Gwiwar Sin Da Birtaniya Ya Kara Taka Rawa
[ad_1]
Yayin da ake kara samun sauye-sauye da tashe-tashen hankula a duk fadin duniya, firaministan kasar Birtaniya Keir Starmer ya kaddamar da ziyarar aiki a kasar Sin, wacce ita ce ta farko da wani firaministan Birtaniya ya kawo Sin cikin shekaru takwas. Kana, Starmer ba shi ne shugaban kasa kadai da ya kawo ziyara kasar Sin kwanan nan ba. Kafar CGTN da ke karkashin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya gudanar da wani binciken jin ra’ayoyin masu amfani da shafin intanet, inda kaso 85.2 bisa dari na masu amsa tambayoyi suka nuna cewa, ziyarce-ziyarcen aiki da manyan jami’an gwamnatin kasashe daban-daban suka kawo kasar Sin sun shaida cewa, cudanyar mabambantan sassa cikin daidaito da dinkewar duk duniya baki daya da ke shafar bangarori daban-daban sun riga sun zama matsaya daya da aka cimma tsakanin kasa da kasa.
Ra’ayin nuna bangaranci, da na bada kariya, gami da ra’ayin nuna babakeren siyasa, sun zama ruwan dare a duk duniya, al’amarin da ya haifar da babbar illa ga tsarin kasa da kasa. A matsayinsu na kasashe membobin dindindin a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, kana, kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, ko a bangaren tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ko kuma a bangaren raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma a kasashensu, ana bukatar karfafa hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin Sin da Birtaniya. Kana kuma, kaso 67.4 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi fatan kasashen biyu za su kara daukar nauyin dake rataye a wuyansu, don tinkarar matsalolin da ke addabar duniya cikin hadin-gwiwa.
An gudanar da wannan binciken jin ra’ayoyin jama’a ne a dandalolin CGTN na harsuna daban-daban, ciki har da Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da kuma Rashanci, inda a cikin sa’o’i 24 aka samu masu amfani da intanet na ketare 9086 da suka bayyana ra’ayoyinsu. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link