An damfari wata mata N603m don nada ta Shugabar NNPC

[ad_1]



Dubun wani mutum ta cika bayan da ya damfari wata mata kudi Naira miliyan 603.4 da cewa zai sa shugaban kasa ya nada ta a matsayin Shugabar Kamfanin Mai na Kasa NNPCL.

Bayan karbar kudin, mutumin tare da wata abokiyar cin mushensa sun yaudari matar gabatar mata da takarda daga  Fadar Shugaban Kasa ta hannun Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a fannin Tsaro a matsayin shaidar nadinta a matsayin shugabar NNPCL.

A ranar Litinin Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta gurfanar da mutumin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke yankin Maitama a Abuja, kan zargin aikata laifuka shida masu alaka da damfara.

Lauyan EFCC, Y. Tarfa, ya shaida wa alkali cewa mutumin mai suna Gidado Ibrahim tare da wata mai suna Halimat Adenike Tejusho wadda yanzu ake nema ne suka hada baki suka karbi kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 603,4000,0000 a hannun wata mai suna Oluseye Yomi-Sholoye, da sunan za su sa a nada ta a kujerar Babban Shugaban NNPCL.

Ya ce wadanda ake zargin sun karbi kudaden ne a cikin wata biyu—watan Agusta zuwa Oktoban shekarar 2024—a matsayin kafin alkalami, inda suka gabatar wa Yomi-Sholoye takardar bugi daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a fannin Tsaro game da nadin ta.

Sai dai bayan karanta masa tuhume-tuhumen, wanda ake zargi ya musanta, inda lauyan EFFCC, Tarfa ta bukaci kotun ta sanya ranar sauraron shari’ar da kuma bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Lauyan wanda ake zargi, B. B Alhaji ya sanar da kotun game da bukatar beli da ya shiga, yana mai cewa duk da cewa lokacin sauraron bukatar bai yi ba, yana rokon a tsare wanda yake karewan a ofishin EFCC maimakon gidan yari.

A karshe alkalin kotun, Mai Sharia Muazu ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan nan na Fabarairu, tare umarnin tsare wanda ake zargin a Gidan Yarin Kuje.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *