NNPP da APC na musayar yawu kan neman Mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus
[ad_1]
Jam’iyyar adawa ta NNPP da kuma APC mai mulki a Jihar Kano, sun shiga musayar yawu kan neman Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo da ya yi murabus.
Tun dai bayan da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, aka shiga nuna wa juna yatsa tsakanin jiga-jigan jami’an gwamnati har ma da magoya bayan ɓangarorin biyu.
A wannan Alhamis ɗin aka jiyo kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Waiya, ya shawartar Mataimakin Gwamnan da ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon rashin bin gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Dabo, Kwamishina Waiya ya ce tafiyar da mulki na buƙatar cikakken aminci da fahimtar juna tsakanin shugabanni.
A cewar kwamishinan, “ci gaba da halartar tarukan Majalisar Zartarwa daga wanda ba ya tare da gwamnati a siyasance na iya zama barazana ga sirrin gwamnati.
“Ra’ayinsa ne rashin bin gwamna Abba zuwa APC, amma babu yadda za a yi wanda ba ya tare da kai ya ci gaba da halartar tarukan Majalisar Zartarwa,” in ji Waiya.
“Wa ya san wanda zai iya bayyanawa muhimman bayanan gwamnati? Mulki yana tafiya ne bisa amana, kuma ba za ka iya yarda da wanda ba ya tare da kai ba.”
Waiya ya ƙara da cewa, a ganinsa, murabus shi ne mataki mafi dacewa kuma mai mutunci da mataimakin gwamnan zai ɗauka a irin wannan hali. “Da ni ne, da na yi murabus cikin da kaina,” in ji shi.
Maganganun kwamishinan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kano, ciki har da sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
NNPP ta yi martani
To sai dai a martanin da jam’iyyar NNPP ta yi dangane da wannan ɗambarwa, ta Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labara wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan ya ajiye aikinsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan damar ci gaba da riƙe muƙaminsa.
NNPP ta ce mataimakain gwamnan na da ikon ci gaba da gudanar da ayyukansa saboda sun yi takara tare gwamnan jihar.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci ɓangaren zartaswa na Jihar Kano da ya daina shiga al’amuran siyasa, ya tsaya kan ayyukan da kundin tsarin mulki ya ba shi damar aiwatarwa.
“Ci gaba da aikin Mataimaikin Gwamna yana da muhimmanci wajen ɗorewar shugabanci a Jihar Kano,” in ji sanarwar NNPP.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa kwamishinan yaɗa labaran ba ya nan lokacin da ake gwagwarmayar kafa gwamnati, don haka ya ja bakinsa ya yi shiru.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link