Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda sama da 400 a Zamfara

[ad_1]



Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen.

Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su tari hanzarinsu.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan farmakin na zuwa ne bayan zanga-zangar lumana da mazauna birnin Gusau suka gudanar a makon da ya gabata kan yadda matsalar tsaro ta ƙara tsananta a jihar.

Ana iya tuna cewa, a ranar Alhamis da ta gabata ce daruruwan mata, galibi tsofaffi da masu juna biyu daga ƙauyen Jimrawa, Kaura Namoda, suka fito kan titi domin nuna adawa da yadda matsalar rashin tsaron ta tsananta a bayan nan.

Mazauna dai sun yi ƙorafin cewa lalacewar hanyoyi a jihar na taimaka wa ’yan ta’adda wajen kai hare-hare, yayin da jami’an tsaro ke samun matsala wajen isa wuraren da ke fuskantar hare-hare  a kan kari.

Da yake ƙarin haske a ranar Litinin game da farmakin da sojoji suka kai a ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar sojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri, an gano kai-komon fiye da ‘yan ta’adda 400 suna shirin kai hari.

Ejodame ya ce: “An yi musu luguden wuta ta sama da ƙasa, inda aka kashe shugabannin ’yan ta’adda da dama da mabiyansu masu yawa.”

Ya ƙara da cewa, “haɗin kan da aka samu tsakanin sojojin sama da na ƙasa ne ya sanya wannan nasarar da muka samu ta zama ta musamman.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *