Mafarkin Nijeriya Na Zuwa Gasar Kofin Duniya Na Dab Da Cika

[ad_1]


Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan zargin amfani da dan wasan da bai cancanta ba a wasan da Nijeriya ta buga da kasar Dimokuradiyar Congo a lokacin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya ta FIFA ta shekarar 2026, wani abu da zai iya sake bude hanyar Nijeriya na zuwa gasar da za a buga a kasashen Amurka, Kanada da Mexico, in ji rahoton PUNCH Online.

DR Congo ta fitar da Nijeriya daga gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka a watan Nuwamba bayan ta yi nasara a bugun fenariti da ci 4-3 a Morocco, sakamakon da ya kawo karshen fatan Super Eagles na zuwa gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA.

Tun daga lokacin ne aka bai wa tawagar Congo damar shiga wasan karshe na gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, inda aka tsara za su fafata da kasar da tayi nasara a wasan kusa da na karshe tsakanin New Caledonia da Jamaica, amma yanzu damarsu ta halartar wannan matakin na iya zama cikin shakku bayan hukumar NFF ta fitar da korafin yin amfani da dan wasan da bai cancanta ba a wasan na watan Nuwamba.

Rahotannin sun nuna cewa tsakanin yan wasan Dimokuradiyyar Congo shida zuwa tara wadanda suka amince su canza kasar da suke wakilta zuwa kasar Congo, ba su cika ka’idojin cancantar da dokar Congo ta tanada ba kafin su wakilci kasar, duk da cewa FIFA ta ce ta wanke yan wasan ne bisa ga cewa suna da fasfo na Congo masu inganci, ana zargin sun kasa soke fasfon kasar da suka taba taka leda a shekarun kuruciya a baya, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar dake Afirka ta Tsakiya, wadda bata yarda da dan wasa yayi amfani da fasfo biyu ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *