Yarinya ta mutu, mai ciki ta haihu a hannun ’yan ta’adda a Neja
Wata yarinya ’yar shekara 14 ta rasu yayin da wata mai juna biyu da aka sace su tare ta haihu a cikin daji a hannun ’yan bindiga a Jihar Neja.
Rahotanni sun ce yarinyar ta rasu ne sakamakon wata cuta da ba a bayyana ba, bayan sun shafe sama da watanni biyu a hannun ’yan ta’adda.
An sace mutanen ne wata biyu da suka gabata daga garin Ibeto na Karamar Hukumar Magama, a wani hari da aka kashe mutane huɗu, tare da jikkata wasu tara, yayin da iyalan waɗanda aka sace ke ci gaba da fuskantar tsananin damuwa sakamakon jinkirin ceto.
An sace Ummi tare da wasu mutum 16 a ranar 1 ga Oktoba, 2025, lokacin da gungun ’yan ta’adda suka afka wa garin Ibeto.
Bincike ya nuna cewa wata daga cikin wadanda aka sace, Safina Arma, ta haihu da namiji a cikin dajin ’yan ta’adda.
Rahotanni sun bayyana cewa Safina na ɗauke da tsohon ciki a lokacin da aka sace ta yayin harin da aka kai wa garin.
Majiyoyi sun ce an sanar da iyalan Ummi da na Safina labarin rasuwar yarinyar da kuma haihuwar jaririn ne a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025.
Haka kuma, wakilinmu ya samu labarin cewa daga cikin mutanen da har yanzu ke hannun ’yan ta’adda akwai Barista Isyaku Danjuma, Nana Firdausi Isah, Shamsiya Jibrin, Suwaiba Ashafa, Hadiza Yusuf, da Basira Yunusa.
Sauran sun hada da Sale Boy, Rashida Sale, Mujida Uccu, Safina Arma, Maryam Arma, Sadiqa Arma, Hassan Isah, Hussaina Isah, Aishatu Isah, Ubaida Yusuf, da Na’ima Uccu.
A harin da aka kai wa garin Ibeto a bainar jama’a a ranar 1 ga Oktoba, 2025, an kashe aƙalla mutum huɗu, yayin da wasu tara suka jikkata.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani dan jarida da ke Kontagora, Kwamared Zakari Y. Adamu Kontagora, ya ce Ummi, wadda shekarunta ke tsakanin 13 zuwa 14, ta rasu ne sakamakon rashin lafiya.
Ya ce: “Daga cikin matan da aka sace a Ibeto, wata mai suna Safina ta haihu jiya Litinin da jaririn namiji. Bayan ita, akwai wasu mata da ke ɗauke da juna biyu a hannun ’yan ta’adda, yayin da wasu kuma ke fama da rashin lafiya.
“Haka kuma, wata yarinya ta rasu ranar Juma’a. Halin da ake ciki ba ya barin mutum ya ce komai face yin addu’a Allah Ya kubutar da su, domin alamu sun nuna hukumomi kamar ba su damu ba.
“Abin takaici, a ranar Juma’a, yarinyar nan Ummi, ’yar mai shekaru tsakanin 13 zuwa 14, ta rasu bayan ta sha fama da rashin lafiya a cikin dajin hannun ’yan ta’adda.
“An sanar da ’yan uwanta jiya Litinin, kuma mutanen Ibeto sun riga sun gudanar da Sallar Ga’ib a kanta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Bayan ita kuma, akwai wasu daga cikin mutum 17 da aka sace da ke fama da tsananin rashin lafiya, musamman mata da ƙananan yara da har yanzu ke hannunsu,” in ji shi.
Zakari Kontagora ya ƙara da cewa waɗanda aka sace sun shafe kusan kwanaki 100 a hannun ’yan ta’adda ba tare da wata tabbatacciyar alamar ceto ba.
Ya ce iyalai da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa sun shiga cikin tsananin tashin hankali sakamakon tsawon lokacin da suka shafe a hannun masu garkuwa da mutane.
’Yan uwana takwas na hannun ’yan bindiga’
A wani ɓangaren kuma, Armayau Gimba, wanda mutum takwas daga cikin iyalinsa aka sace, ya shaida wa Al Jazeera cewa ’yan ta’addan sun tuntube shi inda suka buƙaci ya biya Naira 800,000, tare da kawo jarkokin fetur 10 da kuma galan 10 na man injin.
Ya ce buƙatun sun tilasta masa sayar da babur ɗin da yake amfani da shi wajen noma, amma duk da haka iyalinsa na nan a hannun masu garkuwa da mutane.
Sai dai manoma a ƙananan hukumomin Bangi da Mariga sun shaida wa wakilinmu cewa har yanzu ba su girbe amfanin gonakinsu na bana ba sakamakon karuwar sace-sacen mutane a gonaki.
Wani manomi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an kashe shugaban al’ummar Yarabawa a Bangi kwanan nan yayin da yake girbin amfanin gonarsa.
Ya ce: “Ba mu samu damar girbe amfanin gonakinmu ba. Waken soya yana lalacewa saboda ya bushe. Wake fari ma ya kai lokacin girbi. Abin da muka samu mun ɗan girbe kawai shi ne masara. Muna buƙatar taimako domin talauci yana kara mamaye mu.”
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Nijar, SP Wasiu Abiodun, ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar tare da sojoji da ’yan banga na kara zage damtse wajen ganin an kuɓutar da mutanen da ke tsare.
Haka kuma, Gwamnan Jihar Nijar, Muhammad Umaru Bago, a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025, yayin ganawa da ’yan jarida a Fadar Gwamnati, ya yi kira da a ƙara yin addu’o’i domin kuɓutar da dukkan mutanen jihar da ke hannun ’yan ta’adda, ciki har da sauran yaran Makarantar St. Mary Primary da ke Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara.