Zulum Ya Yi Allah-Wadai Da Fashewar Bam A Maiduguri, Ya Buƙaci A Ƙara Tsaro A Wuraren Ibada
[ad_1]
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da fashewar bam da ya auku a wasu sassan birnin Maiduguri a yammacin ranar Litinin.
Zulum, wanda ke ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da Umrah, ya bayyana harin a matsayin abin takaici, da rashin imani da kuma zalunci kan fararen hula a cikin watan Ramadan.
- Borno Ta Kashe Naira Biliyan 100 Kan Samar Da Tsaro A 2025 – Gwamna Zulum
- Boko Haram Sun Sake Kai Hari Kan Wani Sansanin Sojoji A Borno
A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar, gwamnan ya buƙaci jama’a su ƙara sanya ido musamman a wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a yayin da ake cikin wannan lokaci na bukukuwa.
Ya ce zuciyarsa na tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka jikkata sakamakon fashewar, yana mai jaddada cewa wannan hari abin Allah-wadai ne kuma ba za a lamunci irin sa ba.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa Sojoji da sauran jami’an tsaro suna kan lamarin, tare da buƙatar mutanen gari su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin nutsuwa tare da sanar da jami’an tsaro duk wani abu da suka ga yana da alamar haɗari.
[ad_2]
Source link