Najeriya ce ta bukaci mu kai hari kan ’yan ta’adda a Sakkwato – Amurka
[ad_1]
Sojojin Amurka sun tabbatar da cewa sun kai hare-hare kan mayakan kungiyar ISIS a jihar Sakkwato a daren Alhamis, bayan gwamnatin Najeriya ta nemi taimakon hakan daga gareta.
Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ta ce “an kashe ’yan ta’addan ISIS da dama” a wannan aikin da aka gudanar a ranar Kirsimeti, wanda aka tsara tare da gwamnatin Najeriya. Hare-haren da aka kai a jihar Sokoto sun kasance na farko da sojojin Amurka suka gudanar a Najeriya a karkashin shugabancin Donald Trump.
A wata sanarwa, sashen rundunar Amurka da ke kula da Afirka ya ce: “A bisa bukatar hukumomin Najeriya, sojojin Amurka sun kai hari a jihar Sokoto, inda suka kashe ’yan ta’addan ISIS da dama.”
Shugaban Pentagon, Pete Hegseth, ya kuma yaba da hadin gwiwar da aka samu tsakanin Washington da Abuja, yana mai cewa: “Mun gode da goyon bayan gwamnatin Najeriya da kuma hadin kai a wannan aiki.”
Harin na Amurka ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tashin hankali da hare-haren ta’addanci a arewa maso yammacin Najeriya.
Duk da cewa Shugaba Trump ya bayyana hare-haren a matsayin martani ga hare-haren da ake kai wa Kiristoci, jami’an Amurka sun jaddada cewa aikin ya gudana ne bisa bukatar Najeriya da kuma cikakken hadin kanta.
Trump, a shafinsa na Truth Social, ya bayyana hare-haren da cewa munana ne kuma masu karfi, yana mai cewa ya taba gargadin mayakan da su daina kashe Kiristoci.
“Allah ya albarkaci sojojinmu. BARKA DA KIRSIMETI ga kowa, har ma da ’yan ta’addan da aka kashe,” in ji shi.
Mazauna kauyen Jabo da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar ta Sakkwato dai sun tabbatar da kai hare-haren na Amurka a kusa da kauyen nasu, kodayake sun ce zuwa yanzu babu rahoton mutuwa ko ma jikkata.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link