Tsaro: Gwamnatin Nijeriya Ta Ɗauki Rayukan Mutane Da Muhimmanci – Peter Obi
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta riƙa ɗaukar rayukan mutane a matsayin abu mai muhimmanci tare da ɗaukar matakin gaggawa kan matsalar rashin tsaro a ƙasar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Obi ya yi martani kan rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da masu ibada 100 a wasu coci uku a Jihar Kaduna a ƙarshen mako.
- Mataimakin Ministan Wajen Sin: Nuna Karfin Tuwo Ba Abun Da Zai Haifar Sai Koma Baya
- Jita-jitar Sauya Sheƙa: Gwamna Yusuf Na Ganawar Sirri Da Tinubu A Aso Rock
Ya ce bai kamata ’yan Nijeriya su ɗauki rashin tsaro a matsayin al’ada ba, yana mai cewa yawaitar labaran sace-sacen jama’a na nuna babbar matsalar tsaro da shugabanci.
Obi ya tambayi dalilin da ya sa jama’a ke ci gaba da rayuwa cikin fargaba yayin da wasu hukumomi ke musanta ko jayayya irin waɗannan al’amura.
Ya kuma bayyana cewa irin wannan matsalar ta faru a jihohin Benue, Zamfara, Kano, Neja da Filato, yana mai cewa Nijeriya ba ta yaƙi amma adadin waɗanda ke rasa rayuka ya zarce na wasu ƙasashen da ke yin yaƙi.
Obi ya soki gwamnati bisa kashe kuɗi wajen farfaganda maimakon kare rayuka da al’umma.
Ya kuma jajanta wa mutanen Kaduna da iyalan waɗanda aka sace, yana mai fatan za a kuɓutar da su lafiya, tare da samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
[ad_2]
Source link