Za A Wallafa Jawabin Xi Jinping Game Da Ayyukan Bunkasa Birane A Mujallar Qiushi
[ad_1]
A gobe Juma’a 16 ga watan nan ne a mujallar Qiushi, za a wallafa wani muhimmin sharhi, wato jawabi game da ayyukan bunkasa biranen kasar Sin da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar a yayin taron da kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya a kwanan baya.
Cikin jawabin, shugaba Xi ya bayyana cewa, an taka muhimmiyar rawa a fannin raya biranen kasar Sin, tare da jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa bisa ka’idar bude kofa, ta yadda za a samar wa kasashen duniya dabarun kasar Sin na neman dauwamammen ci gaban birane. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link