Sin Ta Zama Kasuwar Kayayyaki Da Ba Na Sari Ba Ta Yanar Gizo Mafi Girma a Duniya Cikin Shekaru 13 A Jere
[ad_1]
An gudanar da taron ayyukan kasuwanci ta yanar gizo na Sin a birnin Beijing tsakanin raneku 13 zuwa 14 ga watan nan. Taron ya bayyana cewa, darajar cikakken tsarin kasuwancin dijital na Sin ya wuce Yuan triliyan 23.8, wanda hakan ya sa ta ci gaba da zama kasuwar kayayyaki da ba na sari ba ta yanar gizo mafi girma a duniya a tsawon shekaru 13 a jere.
Tun farkon shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 14, Sin ta samu ingantaccen ci gaban kasuwancin yanar gizo, kuma ya zama wani sabon karfi mai habaka sabon karsashin samar da kayayyaki da hidimomi masu karko. Daga cikinsu, an ci gaba da zurfafa hadin gwiwar kasuwannin dijital da na zahiri, inda ayyukan hadin gwiwar masana’antun yanar gizo sama da 1,500 suka shafi kusan kamfanoni dubu 10, matakin da ya habaka masana’antu na gargajiya.
A fagen hadin gwiwa da kasashen waje, yawan kasashe abokan hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” na Sin ya karu zuwa 36, kuma an samu ci gaba a yankunan ba da misali, wanda hakan ya ba duniya damar raba gajiyar kasuwancin yanar gizo na kasar Sin. A fagen cin gajiyar al’umma, kasuwancin yanar gizo ya haifar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 78, ya kuma habaka karuwar ayyukan jigilar kayayyaki cikin sauri da kashi 20% a kowace shekara, yayin da ayyukan samar da hidimomi na dandamalin sarrafa sakwanni ta yanar gizo, da manyan bayanai da makamantansu suka karu cikin sauri. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link