EFCC ta sake gurfanar da Malami, matarsa da ɗansa

[ad_1]



Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC) a ranar Juma’a, ta sake gurfanar da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Abubakar Malami (SAN), tare da matarsa, Asabe Bashir da ɗansa, Abdulaziz, kan zargin laifukan halatta kuɗin haram.

An sake gurfanar da su ne a gaban Mai shari’a Joyce Abdulmalik na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, biyo bayan mayar da shari’ar zuwa hannun sabon Alƙalin.

Yayin da aka ci gaba da sauraron ƙarar, lauyan EFCC, Jibrin Okutepa (SAN), ya sanar da kotun cewa an shirya zaman ne domin sake karanta wa waɗanda ake ƙara tuhume-tuhumen da ake musu.

“Wannan shari’a ta zo gaban mai shari’a a karon farko a safiyar yau. Zan nemi a bar waɗanda ake ƙara su bayyana matsayin su (ko sun amsa laifin ko ba su amsa ba),” in ji shi.

Haka zalika, Okutepa ya nemi kotu ta gyara wasu alƙaluma a cikin tuhume-tuhume na 11 da na 12, inda ya buƙaci a mayar da su Naira miliyan 325 maimakon Naira biliyan 325 a tuhuma ta 11, sannan Naira miliyan 120 maimakon Naira biliyan 120 a tuhuma ta 12.

Bayan da lauyan waɗanda ake ƙara, Joseph Daudu (SAN), bai nuna adawa ba, Mai shari’a Abdulmalik ta amince da buƙatar Okutepa.

Sai dai dukkan waɗanda ake ƙaran sun musanta laifuka 16 da hukumar yaƙi da rashawa take tuhumar su da su, waɗanda suka shafi halatta kuɗin haram.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, wani Alƙali, Mai shari’a Obiora Egwuatu, ya janye daga shari’ar a ranar 12 ga Fabrairu, jim kaɗan bayan an mƙa masa ƙarar da EFCC ta shigar.

Rahoton NAN ya ƙara da cewa, asalin shari’ar tana gaban Mai shari’a Emeka Nwite ne, wanda ya zauna a matsayin Alƙalin lokacin hutu na Kirsimeti da Sabuwar Shekara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *