Hajjin 2025: EFCC ta kama manyan jami’an NAHCON kan zargin almundahanar kuɗi

[ad_1]



Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama Kwamishinan kula da tsare-tsare, Aliu Abdulrazak da daraktan kuɗi, Aminu Y. Muhammed, a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), kan zargin karkatar da kuɗin aikin Hajjn 2025.

An ce an gayyace su ofishin EFCC, amma daga bisani aka tsare su bayan sun kasa mayar da kuɗin da ake zargin sun yi amfani da su ba bisa ƙa’ida ba.

Har zuwa daren ranar Talata, suna hannun hukumar EFCC.

Kamen na zuwa ne bayan ƙorafin da wasu suka yi kan aikata rashin gaskiya wajen kashe wasu kuɗaɗe da aka yi a lokacin aikin Hajjin bana.

A baya-bayan nan, Ƙungiyar Shugabannin Hukumar Alhazai na Jihohi ta bayyana aikin Hajjin ƙarƙashin shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, a matsayin wanda yake cike da kurakurai.

A farkon wannan watan, EFCC ta kuma yi wa wasu manyan jami’an NAHCON tambayoyi, ciki har da Abdulmalik Diggi (mataimakin daraktan lissafi), Sirajo Usman Salisu (mataimakin darakta a ofishin shugaban hukumar).

Sauran sun haɗa da Barista Nura Danladi (mai ba da shawara kan harkokin shari’a), da wani mai bai wa shugaban hukumar shawara na musamman.

Majiyoyi sun bayyana cewa Abdulrazak da Muhammed ana bincikensu kan wata badaƙalar karkatar da kuɗi da ta faru a zamanin tsohon shugaban NAHCON, Ahmad Jalal Arabi.

Da aka tambayi ko za a saki mutanen biyu, wani jami’in EFCC ya ce: “Sun kasa mayar da kuɗin da muka ce su mayar. Ba mu damu ko suna ƙoƙarin mayar da su ba. Abin da muka sani shi ne sai sun dawo da abin da suka ci ba bisa ƙa’ida ba.”

Jami’in ya ƙara da cewa ba a tantance adadin kuɗin ba tukuna.

Shugaban NAHCON na yanzu, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa, shi ne ya kula da aikin Hajjin bana da ya gudana.

Ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ci tura, domin bai amsa kira ba kuma bai mayar da saƙon da aka tura masa ba.

Sai dai NAHCON ta fitar da sanarwa ta hannun Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar yaɗa labarai da wallafa bayanai, inda ta ce hukumar za ta ci gaba da aiki da gaskiya da riƙon amana.

“A matsayinta na hukuma mai daraja, NAHCON tana da alaƙa ta haɗin gwiwa da dukkanin hukumomin gwamnati, ciki har da masu yaƙi da cin hanci da kuma masu sanya ido.

“Wannan haɗin gwiwar ya zama ginshiƙin aikinta, kuma ba za ta kare duk wani jami’i ko tsari da aka samu da laifi ba,” in ji Usara.

Ta kuma roƙi jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa jita-jita kafin a kammala bincike.

“Muna roƙon kowa ya bar hukumomi su kammala aikin bincikensu bisa tsarin doka, ba tare da muzanta wa waɗanda watakila ba su da laifi a kafafen yaɗa labarai ba,” in ji ta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *