Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi
[ad_1]
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa hukuncin daurin shekaru takwas ba tare da zaɓin tara ba, kan laifin luwadi da ɗan wasan kulob dinsa mai karancin shekaru.
Kotun dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad a ranar Laraba ta sami kocin mai suna Hayatu Muhammad da aikata laifin.
Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Sanka ne a ƙaramar hukumar Dala, kuma kotun ta tabbatar da cewa ya aikata laifin har sau biyu a wurare daban-daban.
Da farko dai ya musanta zargin da ake masa.
Sai dai, bayan tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, lauya mai gabatar da ƙara daga Gwamnatin Jihar Kano, Ibrahim Arif Garba, ya kira shaidu guda biyar da suka ba da shaida a kotu.
A bangarensa, wanda ake tuhuma shi kaɗai ne ya ba da shaida don kare kansa.
Bayan nazarin dukkan shaidun da aka gabatar da kuma bayanan shaidu, Mai Shari’a Dahuru ya tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin kamar yadda aka zarge shi.
Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekara huɗu kan kowacce tuhuma, kuma ya bayar da umarnin cewa hukuncin zai fara ne tun daga ranar da aka yanke hukuncin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link