An Harbe Kwamandan Soja Yayin Da Boko Haram Ta Kai Hari Wani Sansanin Soji
[ad_1]
‘Yan ta’addan Boko Haram sun sake kwace wani sansanin soji a Jihar Borno, inda suka kashe kwamandan sansanin da wasu jami’an soja.
Sabon harin ya faru ne a Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno da sanyin safiyar ranar Litinin.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Zulum Kan Faɗaɗa Ilimin Fasaha Da Sana’o’i A Borno
- Wike Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 8.4 Domin Shawo Kan Matsalar Tsaro A Abuja
Wata majiya daga garin ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai hari sansanin sojin ne da misalin karfe 12:30 na dare.
“Sun shigo garin daga ɓangarori da dama sannan suka kaddamar da hari kan sansanin sojin,” in ji majiyar.
Wata majiyar tsaro kuma ta ce, ‘yan ta’addan sun fatattaki sojojin daga sansanin, sannan suka kone wasu motocin soja tare da kwashe makamai da alburusai.
“Ba zan iya bayyana yawan waɗanda suka rasu ba a yanzu, amma abin bakin ciki ne cewa, mun rasa kwamandan sansanin a wannan harin,” in ji ɗaya daga cikin majiyoyin tsaron.
[ad_2]
Source link