Dalilin da ya sa muka ziyarci Obasanjo — Turaki

[ad_1]



Shugaban jam’iyyar PDP) na ƙasa, Taminu Turaki, ya bayyana cewa sun kai wa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ziyara domin neman shawarwari da goyon baya gabanin zaɓen 2027.

Turaki, wanda ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP kwanan nan, ya ziyarci Obasanjo a garin Abeokuta, da ke Jihar Ogun, tare da wasu manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaban Kwamitin Amintattu, Sanata Adolphus Wabara, da wasu tsofaffin gwamnoni.

Ya ce ziyarar wani ɓangare ne na gabatar da sabon shugabancin jam’iyyar ga tsohon shugaban ƙasar.

“Mun zo ne domin gode wa tsohon shugaban ƙasa kan gudunmawarsa ga dimokuraɗiyya, tare da neman shawarwari da jagoranci yayin da muke shirin tunkarar zaɓen 2027,” in ji Turaki.

“Daga shawarwari da ƙwarin gwiwar da muka samu a yau, muna da tabbacin cewa PDP ta shirya tsaf domin komawa kan mulki a shekarar 2027,” in ji shi.

Turaki, ya ce jam’iyyar PDP yanzu ta samu haɗin kai kuma ta shirya tsaf domin tunkarar manyan zaɓuka masu zuwa, ciki har da zaɓen gwamna a jihohin Ekiti da Osun.

Shi ma Shugaban PDP na Jihar Ogun, Abayomi Tella, ya ce ziyarar ta ƙara wa mambobin jam’iyyar ƙwarin gwiwa.

Ya ƙara da cewa ’yan Najeriya sun gaji da rashin kyakkyawan shugabanci kuma suna buƙatar sauyi a zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *