Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20
[ad_1]
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi
Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009.
A yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.
‘Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Morocco ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 sun buga wasan ƙarshe cikin natsuwa da ƙarsashi, cike da ƙwarin gwiwa, lamarin da ya ba da gudunmuwa haƙarsu ta cimma ruwa.
Ɗan wasan gaban Morocco, Yassir Zabiri, shi ne gwarzon wannan karo, inda a cikin minti na 12 da fara wasa ya ci ƙwallon farko ta hanyar bugun tazara, sannan daga bisani ya sake jefa ƙwallo ta biyu bayan hutun rabin lokaci.
Tawagar Argentina, wadda ke neman kofi na bakwai a tarihin wannan gasa, sun yi duk mai yiwuwa wajen riƙe ƙwallo a yayin wasan, amma suka gaza fasa bayan Morocco da ke ƙarƙashin jagorancin Youssef Benchaa.
Morocco dai ta taka rawar gani sosai a wannan gasa, inda ta fara doke Spain, Brazil, Koriya ta Kudu da Amurka, sannan a wasan kusa da ƙarshe ta doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Tawagar Morocco ta yi rashin nasara ne kawai a hannun Mexico a matakin rukuni, amma daga nan ta ƙara ƙaimi suka ci gaba da taka rawar gani har suka ɗaga kofin.
Messi ya jajanta wa ‘yan wasan Argentina
Tauraron ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, ya jajanta wa tawagar Argentina ta ‘yan ƙasa da shekaru 20, bayan rashin nasarar da ta yi a gasar da aka kammala ranar Lahadi a ƙasar Chile.
Messi ya wallafa a Instagram cewa, “Ku saurara, yara!!! Kun taka rawar gani a gasar, kuma duk da cewa mun so ganin kun ɗaga kofin, mun yi murna da abin da kuka ba mu, da kuma alfaharin yadda kuka kare tutar ƙasarmu da zuciyarku.”
Wannan rashin nasara ta ja hankalin tauraron ɗan wasan, wanda ya taɓa lashe gasar ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 tare da Argentina a shekarar 2005.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link