Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki

[ad_1]



Gwamnonin Kano da Katsina da na Jigawa sun shiga wata yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnonin sun zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano wato KEDCO.

A cewar wata sanarwa da Kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na Jihar Kano, Dokta Gaddafi Sani Shehu, ya fitar, an cimma yarjejeniyar ne a yayin taron bunƙasa wutar lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.

Dokta Gaddafi ya bayyana cewa jihohin uku za su yi aiki tare wajen gano sabbin hanyoyin inganta kasuwannin wutar lantarki, tare da kafa tsare-tsaren doka da tsarin haɗin gwiwa don inganta aikin rarrabawa da samar da wuta.

Ya ce, “samun hannun jari a kamfanin FEA zai taimaka wajen ƙarfafa dabarun KEDCO da kuma bunƙasa samar da wutar lantarki a yankin Arewacin Yamma.”

Kwamishinan ya ƙara da cewa jihohin za su kashe naira biliyan 50 wajen aiwatar da ayyukan bunƙasa wutar lantarki da kuma samar da wuta ta hanyoyi daban-daban, ciki har da na tsarin amfani da fasahar samar da wuta da hasken rana.

“Kazalika, za mu yi aiki tare da KEDCO domin rage asarar wuta daga masu amfani a gida, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen samar da wuta ga al’umma,” in ji shi.

An tsara cewa wakilan jihohin za su gudanar da taron kasa da kasa a kowace shekara, sannan su gana sau huɗu a shekara domin duba ci gaban ayyuka da tsara manufofi da karfafa dangantaka a kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *