Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi


An yi garkuwa da Firist na St. Paul Catholic Parish, Agaliga-Efabo, a karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, Rev. Fr. Wilfred Ezemba, a bakin bindiga. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025, a Imane, inda aka ruwaito cewa an kuma sace wasu fasinjoji tare da shi a hanyar Imane-Ogugu Road.

Wannan lamari ya jefa mabiya cocin Katolika a cikin tashin hankali domin zuwa yanzu masu garkuwar ba su tuntubi kowa daga cikin iyali ko mambobin cocin ba. Wani firist a yankin, Fr. Michael, ya bayyana cewa suna cikin rudani, amma suna da kwarin gwiwa cewa addu’o’insu za su taimaka wajen kubutar da abokin aikinsu.

Jami’an tsaro sun fara aikin bincike da ceto, inda rundunar ‘yan sanda, sojoji da Kogi East Neighbourhood Watch (KENW) suka shiga daji suna bin sawun masu garkuwar. Wannan na zuwa ne mako guda bayan wani lauya, Barr. A. B. Shaibu, ya shiga hannun masu garkuwa a yankin kuma aka sako shi bayan iyalinsa sun biya kudin fansa.

Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.

A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.




Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp





Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *