Wadanne Kasashe Ne Ba Su Taba Zuwa Kofin Afirka Ba?

[ad_1]

Kawo yanzu tuni aka buga gasar cin kofin Afirka na shekara ta 2025 wanda kasar Moroko take karbar bakunci, gasar da ake ganin an dade ba a tsara gasa wadda ta ja hankalin magoya baya ba irin wannan.

Hankula tuni suka karkata kan gasar cin kofin Afirka da ake afatawa a Morocco hankali ya fara komawa kan lissafe-lissafen yadda gasar za ta kaya. Wannan ne karo na 35 da ake fafata gasar tun daga watan Fabrailun shekarar 1957 da aka fara babbar gasar ta nahiyar Afirka.

  • Jam’iyyar NNPP Za Ta Yi Gagarumin Tasiri A Zaben 2027 – Kwankwaso
  • Manyan Ƙalubale 5 Da Janar Christopher Musa Zai Fuskanta Domin Yin Nasara

Kasashe 24 ne ke fafatawa a gasar ta AFCON ta bana wadda aka fara daga ranar 21 ga watan Disamban 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026. To sai dai akwai wasu kasashe guda 10 da ba su sami gurbin shiga gasar ba ko kuma ma ba su taba zuwa gasar ba a tsawon rayuwarsu. Wadannan kasashen su ne kamar haka:

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Chad, Djibouti, Eritrea, Eswatini, Lesotho, São Tomé da Príncipe Seychelles, Somalia, Sudan ta Kudu

An dai karkasa tawagar kasashe 24 da ke fafatawa a gasar ne zuwa rukunoni guda shida, inda kowane rukuni ke dauke da tawagar kasashe guda hudu a cikinsa kuma tawagogin za su fafata a tsakaninsu domin fitar da guda biyu da suka yi zarra a matakin farko.

Kuma kamar yadda yake a tsare, kasashen ne za su tsallaka zuwa zagaye na biyu ko kuma zagayen da ake kira ‘yan 16, inda za a fara fafata kifa daya kwale kamar yadda ake yi a kowacce gasa.

Kasar Morocco ce ta karbi bakuncin gasar ta bana, inda ake tunanin za a nishadu ganin irin yadda kasar ta zuba jari matuka a harkar wasanni, musamman ma harkar kwallon kafa, inda har ta samu shiga cikin kasashen da za su yi hadaka wajen karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2030.

Daga cikin sauyin da aka samu a gasar ta bana, akwai canjin lokaci, inda maimakon tsakanin watan Yuni zuwa Yuli da aka saba, a bana za a fara gasar ne a watan Disamba, matakin da aka dauka saboda shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da ake yi.

Kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara, lamarin da bai yi wa wasu masoya kwallon kafa musamman a nahiyar Afirka dadi ba.

Kanu, Salah, Drogba, Da Manyan ‘Yan Wasa

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *