’Yan ɗaurin aure 7 sun rasu a hatsarin mota a hanyar Borno

[ad_1]



Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa kan rasuwar ’yan ɗaurin aure bakwai daga ƙauyen Lawanti da ke Ƙaramar Hukumar Akko, waɗanda hatsarin mota ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri domin halartar ɗaurin aure.

A wata sanarwa da Darakta Janar na Harkokin Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya ce lamarin rashi ne mai taɓa zuciya.

Ya ce wannan rasuwar ta shafi iyalan mamatan, al’ummar Lawanti, Ƙaramar Hukumar Akko da kuma ɗaukacin Jihar Gombe.

Gwamnan, ya ce rasuwar ta zo ne ba zato ba tsammani, kuma ta girgiza jama’a sosai.

Ya jajanta wa iyalan mamatan, ciki har da Dagacin Jalingo, Bello Hassan Babangida, wanda ya rasa ’yar uwarsa da ’yar yayarsa; Idris Lawanti Maigari, wanda ya rasa ’yarsa; da kuma Kansilan Akko, Idris A. Isah Lawanti, wanda shi ma ya rasa ’yan uwansa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan kurakuransu, Ya karɓi ayyukan alherinsu, kuma Ya sanya su a Aljanna Firdausi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *