Hadaddun Lemukan ‘JUICE’
[ad_1]
Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake hada lemummuka:
- Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Taurarin Dan Adam Na Sadarwar Intanet
- An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce
Hade-haden Lemon Shayi:
Abubuwan da a ake bukata:
Kankana, Kokumba, Sitoru Beri Na Ruwa, Lemo, Tea Bag, Danyar Citta, Abarba, Lemon Juice, Na’a-na’a:
Yadda za a hada:
Da farko za a wanke kankana da danyar citta sai a nika su, sannan a tace a zuba a cikin tukunya sai a dora akan wuta, sannan a wanke Abarba da Kokumba sai a yanka a zuba a cikin tukunya, sannan a sa tea bag din a ciki idan ya tafasa sai a sauke a wanke Lemo a matse a wata roba za a samu roba mai kyau sai a tace lemon da aka matse da hade haden lemon shayin a ciki sai a sa Sitoruberi na ruwa da lemon juice a ciki sannan a sa ganyan na’a-na’an kadan a ciki za a ji ya yi kamshi sosai. Asha dadi lafiya.
Lemon tsamiya:
Abubuwan da za a tanada:
Tsamiya, Citta danya, Suga, Filebo :
Yadda za a hada:
Da farko za a wanke tsamiya sai a dafata a tace sannan a wanke danyar citta a nika ta a samu roba mai kyau a tace tsamiya tare da cittar a zuba suga da filebo a juya sosai asa a firji ko a sa masa kankara. A sha dadi lafiya.
[ad_2]
Source link