Bangaren Dawowa Na Kumbon Shenzhou-20 Ya Dawo Doron Kasa
[ad_1]
Bangaren dawowa na kumbon Shenzhou-20 ya sauka ba tare da ‘yan sama jannati ba, a wurin saukar kumbuna na Dongfeng dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta ta arewacin kasar Sin da misalin karfe 9:34 na safiyar yau Litinin.
Hukumar kula da harkokin sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta ce nazarin da aka yi bayan saukarsa, ya tabbatar da cewa komai na jikin kumbon na nan, haka ma dukkan kayayyakin dake cikinsa, inda ta bayyana aikin dawowarsa a matsayin mai cikakkiyar nasara.
A ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2025 ne kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou-20 dauke da ‘yan sama jannati 3 zuwa da’irar da aka tsara domin aiki na tsawon watanni 6.
Sai dai, kumbon Shenzhou-20 da aka tsara zai dawo dauke da ‘yan sama jannatin 3 zuwa doron kasa a ranar 5 ga watan Nuwamba, bai cimma sharudan dawowa cikin aminci ba.
An samu wasu kananan tsaga a jikin bangaren dawowar kumbon, wadanda ake ganin sun samu ne saboda burbushi da wasu abubuwan dake akwai a sararin samaniya. (FMM)
[ad_2]
Source link