Sojoji Sun Daƙile Harin Jirgi Maras Matuƙi Na Ƴan Boko Haram A Borno
[ad_1]
Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) sun daƙile wani harin da ƴan Boko Haram suka kai ta amfani da jirgin sama maras matuƙi (drone) a yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno, inda suka kuma ƙwato tarin kayan aikin ƴan ta’adda da suka haɗa da tutoci, da alamomi, da wasu muhimman kayan soji da na dabarun aiki.
Jami’in yaɗa labarai na dakarun haɗin gwuiwa (JTF) Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Ya ce Sojojin sun fuskanci harin ne yayin da suke ci gaba da kai farmaki bayan sun kammala ayyukan leƙen asiri da aka tsara a wasu sansanonin ƴan ta’adda da suka haɗa da Chilaria, da Garin Faruk, da Abirma a ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026.
- Ƴan Boko Haram Sun Nemi Dalar Amurka $300,000 Domin Sakin Mutane Biyu
- Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo
Sanarwar ta ce rundunar, tare da goyon bayan ɓangaren sama na OPHK, ta gudanar da sa ido da bincike na tsawon lokaci, lamarin da ya ba su damar bibiyar motsin ƴan ta’adda a kan lokaci, da hana musu samun sakewa, da kuma ƙara daidaito da ƙarfin gwuiwa wajen aiyukan ƙasa.


A yayin sumamen, Sojojin sun ƙwato rediyon Baofeng, da wayoyin hannu, da sinƙi biyar na harsashin bindigar AK-47, da harsashi mai girman 7.62×39mm da 7.62mm NATO, tutocin Boko Haram/ISWAP, da alburusai na 12.7×108mm, daga injinan niƙa na dizal, da kayan asibiti da hatsi da dama, da wata motar ɗaukar kaya, da ma’adanar kayan aiki a ƙarƙashin ƙasa, da kuma ma’ajiyar man fetur da mai, matakin da ya rage wa ƴan ta’adda ƙarfin aiki da dabarunsu.

[ad_2]
Source link