Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika
[ad_1]
Cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta Sin (CDC) ta fara kwas din horon fasahar gwaje-gwaje a kasashen waje a ranar 3 ga wata a hedkwatar CDC ta Afirka. Masana daga gwamnatocin Sin da Afirka da fannin kiwon lafiya, da kuma dalibai 30 daga kasashen Afirka 16, sun halarci bikin bude horon.
An bayyana cewa, wannan horon zai dauki tsawon makonni 3, inda cibiyar Africa CDC za ta taimaka wajen gudanar da shi. Fannonin horon sun hada da binciken kwayoyin cuta, da parasite, da gwajin cutar sida, nazarin kwayoyin halitta wato DNA, da ilimin halittu, da sa ido kan juriyar magunguna, da sauran fannoni masu muhimmanci. Manufar ita ce, horar da daliban da ma’aikatan gwaje-gwaje na Afrika CDC da na kasashe daban daban na Afirka, ka’idoji da kuma fasahohin gwaje-gwaje, don samar da kwararrun ma’aikata ga dakunan gwaje-gwaje da kasar Sin ta ba da taimakon ginawa a kasashen Afirka.(Amina Xu)
[ad_2]
Source link