Kamfanin Sin Ya Bude Babban Titin Nairobi Kyauta Ga Masu Ababen Hawa Da Suka Makale Saboda Ambaliya

[ad_1]

Kamfanin kasar Sin mai kula da babban titin Nairobi, ya bude hanyar kyauta domin taimakawa masu ababen hawa isa wuraren da za su je, bayan mamakon ruwan sama da aka yi da yammacin jiya, ya haifar da cunkoson ababen hawa mai tsanani a birnin.

Ruwan da aka fara da misalin karfe 5 na yamma agogon kasar, ya tsananta cikin dare, inda ya cika magudanan ruwa, ya mamale manyan hanyoyi, inda gomman motoci suka makale. Dubban mutane ne suka gaza yin zirga-zirga, inda komai ya kusan tsayawa cik a birnin.

Biyo bayan haka ne babban titin Moja ya ba masu ababen hawa damar bin titin kyauta, ba tare da karbar ‘yan kudin da ake karba na kula da titin ba. Daruruwan direbobi ne suka amfana da hakan, inda suka yabawa wannan taimako da ya ba su damar komawa gida lami lafiya. (Mai fassara: FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *