Sin Ta Zamo Abokiyar Cinikayyar Kasashen Tsakiyar Asiya Mafi Girma A 2025


Ma’aikatar cinikayya ta Sin, ta ce a shekarar 2025 da ta gabata, Sin ta kasance abokiyar cinikayyar kasashen yankin tsakiyar Asiya mafi girma, lamarin da ya bude wani sabon babi na bunkasa huldar tattalin arziki a shiyyar. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar, sun nuna yadda darajar cinikayya tsakanin sassan biyu ta kai dalar Amurka biliyan 106.3, adadin da ya karu da kaso 12 bisa dari a mizanin shekara-shekara, wanda kuma ya dara na shekarar 2024 da kaso maki shida bisa dari.

Alkaluman sun kuma nuna cewa, darajar fannin fitar da hajoji daga Sin zuwa kasashen shiyyar ya kai dala biliyan 71.2, kuma fannonin dake kan gaba su ne na manyan injuna, da kayayyakin laturoni, da na manyan fasahohi, yayin da darajar hajojin da ake shigowa da su kasar Sin daga kasashen yankin na tsakiyar Asiya ta kai dala biliyan 35.1, ciki har da hajojin sinadarai, da karafa da albarkatun gona.

Fannin cinikayya tsakanin sassan biyu ta yanar gizo shi ma ya bunkasa cikin sauri, sakamakon kyautatuwar tsarin safarar kayayyaki, da na biyan kudade ta intanet, da kaddamar da dandalin ingiza hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da shiyyar tsakiyar Asiya a birnin Nanjing.

Har ila yau, ma’aikatar ta ayyana hadin gwiwa mai karko karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da muhimman ayyuka na hade sassan biyu, da raya fannin kirar kayayyakin ayyukan masana’antu, da amfani da ma’adanai marasa gurbata yanayi, da tsarin noma na zamani, a matsayin ginshikan da suka ingiza fitar da hajojin Sin zuwa shiyyar tsakiyar Asiya, tare da tallafawa wajen farfado da matsayin masana’antu, da tattalin arzikin kasashen shiyyar tsakiyar Asiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *