Yadda Ake Haɗa Miyar Uwaidu

[ad_1]

Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haɗuwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai kawo muku yadda ake haɗa miyar Uwaidu:

Abubuwan da ake buƙata:

Nama, Uwaidu, Tattasai, Tumatur,  Kayan yaji, Daddawa, Alayyahu, Manja, amagi, Gishiri, Kori, Albasa:

Yadda ake haɗawa:

  • Obi Na Sauya Jam’iyya Kamar ‘Yan Wasan Firimiyar Ingila – Bwala
  • Mutum 10 Sun Shiga Hannu Bisa Zargin Fashi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Jigawa

Da farko uwargida za ki tafasa namanki, na rago ne, ko na shanu ne ,ko na kaza ne, idan kuma haɗa su za ki yi kamar na rago da na kaza duk za ki iya, sai ki zuba su a tukunya ki wanke su, sannan ki kawo gishiri da ɗan magi da kori da albasa ki zuba ki ɗora ki tafasa shi, idan ya yi daidai yadda kike buƙata  sai ki sauke shi ki zuba mai a tukunyar da za ki yi miyar sannan  ki kwashe ki soya shi, idan ya soyu sai ki kawo kayan miyanki tattasai da tumatur da taruhu idan kina so wanda dama kin jajjaga su ki zuba ki zuba yankakkiyar albasar ki, sannan ki kawo dakakkiyar daddawa ki zuba, ki ɗan soya su sama-sama.

Daga nan sai ki kawo ruwan tafasasshen naman ki zuba, ki zuba magi, gishiri, kayan yaji, kori ki juya su, ki rufe kibar shi ya tafasa, sai ki kawo Uwaidu ki zuba wanda dama kin wanke shi, kin gyara shi kuma kin tafasa shi da ƴar kanwa ki zuba shi, ki bar shi ya ɗan dahu sannan ki kawo alayyahu wanda shi kin gyara shi kin kuma yanka shi ki zuba kiɗan bar shi ya dahu.

Gaskiya miyar ta haɗu ga kyau ga daɗi. Za ki iya ci da tuwon semo, sakwara da sauransu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *