’Yan bindiga sun kashe uban garin Dalijan a Sakkwato
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari garin Dalijan a Ƙaramar Hukumar Binji, a Jihar Sakkwato, inda suka kashe uban garin, Alhaji Ibrahim Magaji Tanko.
Bayan kashe shi, maharan sun sace shanu, awaki, tumaki da kaji, tare da kayan abinci masu yawa.
Ƙaramar Hukumar Binji tana iyaka da Tangaza da Gudu, yankunan da Lakurawa suka matsawa da kai hare-hare.
Wannan lamari ya haddasa tashin hankali da firgici a yankin.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Binji, Alhaji Dikko Nabunkari, ya aike da ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, ya kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali.
Ya ce: “Allah Ya gafarta masa, ya bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.”
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link