Ya Kamata Sin Da Kanada Su Kiyaye Dangantakarsu Ta Mutunta Juna Da Samun Ci Gaba Tare
[ad_1]
“Za a bude sabuwar kofar hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Kanada. Sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da Sin da Kanada suka kulla tare, ta haifar da alherai ga kasashen biyu da ma duniya baki daya”…… Wadannan kalmomin yabo ne da kafofin watsa labarai na kasa da kasa suka rika yadawa, game da ziyarar aikin da firaministan Kanada Mark Carney ya gudanar a kasar Sin, tsakanin ranakun 14 zuwa 17 ga watan nan.
Wannan ne karon farko da firaministan Kanada ya sake gudanar da ziyara a Sin, tun bayan karon karshe shekaru 8 da suka gabata. A yayin ziyarar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaminista Carney, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su zama abokai domin mutunta juna, da samun ci gaba tare, da amincewa juna da kuma hadin gwiwa, inda wannan tsokaci ya samar da jagorancin tsare-tsare, da zai zama sabuwar alkibla ga dangantakar bangarorin biyu.
Ban da haka kuma, bangarorin biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, ta ganawar shugabannin Sin da Kanada, inda suka cimma matsaya daya, game da inganta sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Kanada, da inganta cimma sakamako a fannoni kamar na manyan ayyukan raya tattalin arziki, da cinikayya, da makamashi, da harkokin kudi, da kuma musayar al’adu da cudanyar jama’a, tare da sa hannu kan takardun hadin gwiwa guda 8, wadannan ayyukansu suka kara karfafa kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Kanada.
Masana sun yi nuni da cewa, a halin yanzu, manufar diflomasiyyar da Kanada ke aiwatarwa game da kasar Sin na tattare da nuna ’yancin kai, da sanin ya kamata da kuma aiki tukuru. Sakamakon da aka samu dangane da ziyarar aikin firaminista Carney a Sin, da kuma ci gaban da dangantakar Sin da Kanada ke samu, zai haifar da karin kuzari mai kyau ga duniya mai cike da sauye-sauye.
Bugu da kari, game da huldar Sin da Kanada, bana shekara ce ta musamman. Inda a bana Sin ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15, kuma Kanada ita ma za ta aiwatar da sabon kudurin kasafin kudi, inda kasashen biyu suke fuskantar ayyuka masu muhimmanci na gina tattalin arziki da bunkasa rayuwar al’ummunsu.
A cikin wannan sabon mafari, bisa jagorancin matsayin dangantakar abokantaka a fannoni guda hudu, ta hanyar kara amincewa da juna, da kawar da tsoma baki, da zurfafa hadin gwiwa, Sin da Kanada za su iya sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakaninsu lami lafiya. Wannan ba wai kawai ya dace ne da muradun bai daya na bangarorin biyu ba, har ma zai samar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba da wadata a duniya baki daya. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link