Facebook Ya Cika Shekaru 22 Da Kafuwa
[ad_1]
A yau Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026, kafar sada zumunta ta Facebook ta cika shekaru 22 da kafuwa, tun bayan ƙirƙirarta a shekarar 2004.
An kafa Facebook ne a ranar 4 ga Fabrairu, 2004, a Jami’ar Harvard da ke ƙasar Amurka, ta hannun Mark Zuckerberg tare da wasu abokansa huɗu da suka haɗa da Eduardo Saverin da Andrew McCollum da Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes.
- Mutane 597 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Cikin Wata 1 — FRSC
- EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Bisa Zargin Wulaƙanta Takardun Naira
Da farko, an samar da Facebook ne domin haɗa ɗaliban Jami’ar Harvard, amma daga bisani aka faɗaɗa amfani da shi zuwa sauran jami’o’i, kafin daga ƙarshe ya bunƙasa zuwa kafar sada zumunta ta duniya.
Zuwa shekarar da muke ciki ta 2026, Facebook na da fiye da mutane biliyan 3 da ke amfani da shi a kowane wata a faɗin duniya, lamarin da ya sanya shi zama ɗaya daga cikin manyan shafukan sada zumunta mafiya yawan masu amfani da shi.
Facebook na ƙarƙashin kamfanin Meta, wanda kuma yake kula da wasu kafafen sada zumunta kamar Instagram da WhatsApp da Messenger. A cewar bayanan kamfanin, dandalin na tara mutane sama da biliyan 3.5 masu amfani da shi a kowane wata.
A cikin shekaru 22 da kafuwarsa, Facebook ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya yadda mutane ke sadarwa da gudanar da harkokin kasuwanci da yaɗa labarai, tare da tasiri mai girma a fannoni kamar siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Sai dai kuma, Facebook ya sha fama da fuskantar suka a lokuta daban-daban, musamman kan batutuwan da suka shafi adana sirri da tsaron bayanai da yaɗa labaran ƙarya, duk da cewa kamfanin na cewa yana ɗaukar matakai domin magance matsalolin.
[ad_2]
Source link