Farfesa Mohammed Inuwa Ja’afar ya zama sabon shugaban jami’ar Kashere

[ad_1]



Farfesa Mohammed Inuwa Ja’afar ya zama sabon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK) da ke Jihar Gombe, bayan Hukumar Gudanarwar jami’ar ta amince da naɗinsa.

An yanke shawarar naɗa shi ne a taro na musamman karo na 10 da Majalisar Jami’ar ta gudanar a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2026.

Sanarwar da Babbar Jami’ar Hulɗa da Jama’a, Janet Ibrahim Ezekiel, ta fitar ta ce Shugaban Majalisar Jami’ar, Farfesa Williams Olushola Aderounmu, ya bayyana cewa Farfesa Ja’afar ne ya fi kowa cancanta a cikin ’yan takara 20 da suka nema.

A cewarsa, Farfesa Ja’afar ne ya samu maki mafi yawa a lokacin tantancewar da Majalisar ta gudanar.

Farfesa Ja’afar malami ne a fannin Microbiology a Sashen Microbiology, Faculty of Life Sciences, Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Jihar Adamawa.

Shugaban Majalisar ya nuna ƙwarin gwiwar cewa sabon Shugaban Jami’ar zai ɗaga martabar jami’ar, ya bunƙasa harkokin ilimi da kuma inganta ayyuka.

Da wannan naɗin, Farfesa Mohammed Inuwa Ja’afar ya zama Shugaban Jami’a na huɗu a tarihin Jami’ar Tarayya ta Kashere tun bayan kafuwarta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *