Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Rasha Ta Kafar Bidiyo

[ad_1]

A yau Laraba 4 ga wannan wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta kafar bidiyo a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya jaddada cewa, bana shekara ce ta kaddamar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, da more sabuwar damar samun ci gaba tare da kasa da kasa ciki har da kasar Rasha. Kazalika, bana shekara ce ta cika shekaru 30 da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Rasha, da cika shekaru 25 da daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Rasha, kana shekara ce ta kaddamar da aikin hadin gwiwa na bada ilmi a tsakanin Sin da Rasha. Ya kamata bangarorin biyu su yi amfani da damar, da yin mu’amala tsakanin manyan jami’ai, da kara yin hadin gwiwa a dukkan fannoni, da daukar nauyin da ke wuyan manyan kasashe, da kuma tabbatar da raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

A nasa bangare, Putin ya bayyana cewa, kasar Rasha ta nuna karfin zuciya ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin a sabuwar shekara. Ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da nuna goyon baya ga juna a fannonin tabbatar da ikon mallaka, da tsaron kasa, da neman cimma burin samun bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da sa kaimi ga yin mu’amala da juna a fannonin ba da ilmi da al’adu da sauransu don amfanar da jama’arsu baki daya.

Kasar Rasha tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a zauren MDD, da kungiyar SCO, da kungiyar BRICS da sauransu don sa kaimi ga samar da gudummawa wajen daidaita harkokin kasa da kasa baki daya. Hakazalika, kasar Rasha za ta nuna goyon baya ga kasar Sin wajen gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC da za a gudanar a birnin Shenzhen na kasar Sin. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *