Yawan Hatsin Da Aka Girba A Kasar Sin Ya Kai Kilogiram Biliyan 715 A Bara
[ad_1]
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira wani taron manema labarai da safiyar yau Laraba 4 ga watan Fabrairu, inda aka gabatar da yadda aka gudanar da ayyukan zamanantar da sana’ar noma da yankunan karkara, gami da farfado da kauyukan kasar daga dukkan fannoni. Taron ya kuma ce, a shekarar da ta gabata wato 2025, an gudanar da ayyukan da suka shafi sana’ar noma da yankunan karkara gami da manoma yadda ya kamata, inda aka haye wahalhalu daban-daban, ciki har da munanan bala’u daga indallahi, da kammala ayyukan shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 cikin nasara.
Har wa yau, kasar Sin ta samu babban ci gaba a bangaren samar da amfanin gona, inda a cikin jerin shekaru 2 da suka gabata, yawan hatsin da aka girba a kasar Sin ya zarce kilogiram biliyan 700, kana, wannan adadin ya kai kilogiram biliyan 714.9 a shekara ta 2025, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi. Sai dai kuma yawan waken soya da aka girba a kasar ya zarce tan miliyan 20 a cikin jerin shekaru 4 da suka gabata, yayin da adadin naman da aka samar ya zarce tan miliyan 100 a karo na farko. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link