Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Sun Jima Suna Kitsa Karairayi
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce sassa masu tsattsauran ra’ayi na kasar Japan, sun kwashe tsawon lokaci suna kitsa karairayi. Guo ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, dangane da ikirarin da wasu Japanawa suka yi, cewa kasarsu na da son zaman lafiya, suna masu cewa zargin da kasar Sin ta yi wa Japan din bai dace da hakikanin shaidu ba.
Guo ya kara da cewa, sassan masu tsattsauran ra’ayi na kasar Japan, suna bayyana yakin danniya da Japan din ta kaddamar kan kasashen Asiya makwaftanta, a matsayin wai na “’Yantar da Asiya”, suna kaskantar da munin kisan kiyashin birnin Nanjing, inda suke kiransa da “Abun da ya faru a Nanjing”, da kokarin maida tawagar soji ta 731 ta Japan da ta aikata munanan gwaje-gwajen kwayoyin cututtuka kan al’umma a matsayin hukumar binciken lafiya, da nuna cewa aikin tilas da dakarun na Japan suka tursasa fararen hula aikatawa da radin kansu suka shiga, da nuna matan da aka tilastawa aikata karuwanci sun yi hakan ne bisa ganin damar kansu. (Saminu Alhassan)