HOTUNA: Ɗan Ganduje Ya Ziyarci Kwankwaso A Kano

[ad_1]

Abdul-Aziz Umar Ganduje, ɗan tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke Miller Road a ranar Alhamis.

Hotunan da mai taimaka wa Kwankwaso a harkar yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ya wallafa a Facebook sun nuna Abdul-Aziz sanye da kayan farin kaya da jar hula.

  • GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
  • Taron Cika Shekaru 55 Na “Diflomasiyyar Ping-Pong” Ta Sin Da Amurka Ya Gudana A Amurka

Kwankwaso tare da Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ne, suka tarbe shi.

Ba a bayyana dalilin ziyarar ba.

Ziyarar ta jawo hankalin jama’a saboda Kwankwaso da mahaifin Abdul-Aziz sun daɗe ba sa ga maciji da juna a siyasa.

Kwankwaso
Kwankwaso
Kwankwaso
Kwankwaso

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *