’Yan sanda sun kama ɗan haya kan zargin kisan mai gida
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wani ɗan haya mai suna Bello Abubakar, mai shekara 37, kan zargin kashe mai gidansa, Maryam Hassan, a Unguwar Arawa a cikin garin Gombe.
’Yan sanda sun ce, lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na safe a Unguwar Arawa a, Gombe.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya ce wani mutum nagari ne ya kai rahoto cewa, an sami wata mata mai suna Maryam Hassan, mai shekara 38, kwance a gaban gidanta cikin jini tare da munanan raunuka a kai.
Ya ce, jami’an ofishin ’yan sanda na Gombe Division sun gaggauta zuwa wajen da abin ya faru, inda suka kai ta asibiti, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarta.
“Binciken farko ya kai ga kama wanda ake zargi, Bello Abubakar, wanda ɗan haya ne a gidan marigayiyar, domin yi masa tambayoyi,” in ji sanarwar.
Rundunar ta ƙara da cewa, an gano wasu kayayyakin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifin a hannun wanda ake zargin, ciki har da turmi guda ɗaya, kujera guda ɗaya, bokiti guda ɗaya, riga da ake zargin ta jiƙe da jini, da kuma wayar salula ƙirar Redmi 15C ta marigayiyar da aka samu a hannunsa.
DSP Abdullahi ya ce, daga bisani wanda ake zargin ya amsa laifin, kuma an miƙa shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin zurfafa bincike.
Ya tabbatar wa al’umma cewa, rundunar za ta bi diddigin shari’ar yadda ya kamata.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin inganta tsaro a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link