Kasar Sin Ta Yi Tasiri Sosai Wajen Bunkasar Sashen Fitar Da Hajoji A Duniya
[ad_1]
Yayin da shekarar nan ta 2025 ke daf da karewa, alkaluma na nuna yadda sashen fitar da hajoji na kasar Sin ya kara bunkasa, wanda hakan ke nuni ga sauyin da ake samu a fannin tsarin cinikayyar kasa da kasa, kuma ko shakka babu, harajin da wasu sassa suke ta kakabawa bai dakile cikin fannin fitar da hajoji na kasar Sin ba.
Duk da yadda Amurka ke kara aiwatar da ajandarta, ta kakaba haraji, da kariyar cinikayya, cikin watanni 11 na farkon shekarar nan ta 2025, hajojin Sin sun shiga kasuwannin kasa da kasa da babban rinjaye, sama da wadanda kasar ta shigo da su, har ma rarar hakan ta kai kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.076, adadin da ya haura dala tiriliyan daya a karon farko a tarihi. Ana iya cewa juriyar tattalin arzikin Sin dangane da wannan rarar cinikayya, ta shaida kasancewar kasar babban jigon sarrafa hajoji a duniya, baya ga yadda kasar ke kara bude kofofinta ga bukatun sassan kasa da kasa, ciki har da masu sayayya na Turai, da kudu maso gabashin Asiya, da ma sauran sassan kasashe masu tasowa.
Kasar Sin ta fadada kofofin cinikayyarta zuwa kasuwannin Turai, da kasashe membobin kungiyar ASEAN, inda ta zamo ja-gaba a fannin sarrafa hajoji irin su injuna, da kayan laturoni, da na samar da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa. Kuma hakan ya baiwa kasar damar samun riba mai gamsarwa daga abokan cinikayya, da fadada hulda mai inganci.
A daya hannun, kasar Sin tana ta gaggauta aiwatar da matakan fadada shigo da hajoji daga mabanbantan sassa, musamman kayayyakin albarkatun gona da na abinci. Wanda hakan wata hikima ce ta kaucewa dogaro da sashe daya, don gujewa babakere da shigar da siyasa cikin harkokin cinikayya da kasuwanci irin wanda aka gani yana faruwa a shekarun baya bayan nan daga wasu sassa.
A wurin tarin kasashe masu tasowa, fadadar hada-hadar fitar da hajojin Sin wata babbar dama ce ta samun sauki a kasuwanni. Domin kuwa ababen hawa masu aiki da lantarki masu rahusa, da fasahohin samar da lantarki ta hasken rana, da injunan sarrafa hajoji masu kunshe da fasahohin dijital, na share fagen gaggauta bunkasa masana’antunsu, da cika burin kare muhalli da inganta sarrafa hajoji.
Babban abun tambaya a nan shi ne, shin ko sauran sassan kasa da kasa za su rungumi kasar Sin a matsayin abokiyar tafiya, ko za su rika kallonta a matsayin abokiyar hamayya? Ko ma dai yaya ta kaya, tuni gaskiya ta bayyana cewa, makoma mai dorewa ta cinikayyar kasa da kasa a nan gaba, ta ta’allaka ne ga kwazon fadada cinikayya, da zuba jari, da kirkire- kirkire, da kyankyashe sabbin masu basira, ba wai ta hanyar buga haraji ko matsin lamba ba! (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link