Sauya Sheƙa: Kwamishinoni Na Murabus Daga Muƙamin Gwamna Yusuf

[ad_1]

Air Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya) ya yi murabus daga muƙamin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano.

Bayanin murabus din na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, wacce aka sanya wa hannu a ranar 26 ga Janairu, 2026.

A cikin wasikar, Kwamishinan mai murabus ya nuna godiyarsa ga gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa, inda ya naɗa shi a matsayin Kwamishina.

Ya bayyana cewa, shawararsa ta yin murabus ta biyo bayan abubuwan da suka faru kwanan nan a siyasance, yana mai cewa, ya yanke shawarar ne domin ci gaban jihar da kuma gwamnati.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *