Shirye-Shiryen Cinikayya Tsakanin Sin Da Canada Ba Ta Da Nasaba Da Wata Kasa

[ad_1]

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce shirye-shiryen da aka yi tsakanin kasar da Canada domin shawo kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, ba a yi su don wata kasa ba, kuma za su yi amfani ga samar da zaman lafiya da wadata a duniya.

Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Litinin, biyo bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na sanya harajin kaso 100 kan kayayyakin Canada dake shiga kasarsa, saboda farfadowar dangantakar cinikayya tsakaninta da kasar Sin

A cewar Guo, ra’ayin kasar Sin shi ne, dukkan kasashen duniya su tafiyar da dangantaka a tsakaninsu bisa moriyar juna maimakon nasara bangare daya, kuma cikin hadin-gwiwa maimakon ta hanyar fito-na-fito.

Da yake martani game da ziyara ta baya-bayan nan da tawagar Amurka, karkashin jagorancin dan majalisa mai wakiltar Michigan John Moolenaar ta yi a kasashen tsakiyar Amurka, inda dan majalisar ya yi wasu furuci na batanci kan kasar Sin, kakain ya ce Sin tana adawa da ’yan siyasar Amurka su rika nuna yatsa kan mu’amala ta yau da kullum dake tsakaninta da kasashen yankin tsakiyar nahiyar Amurka. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *