Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

[ad_1]


Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Malam Dikko Radda ta shirya taron tattalin arziki da zuba jari wanda ya gudana a Jihar Katsina.

Taron dai ya gayyato masu ruwa da tsaki a ciki da wajen Nijeriya domin zuba hannu jari a ban-garori daban-daban, musamman sha’anin wutar lantarki da ma’adanai, inda aka yi wa taron take da ‘Gina Gobanka Ta Fuskar Tattalin Arzikin Katsina’.

An gudanar da taron ne na wuni biyu a dakin taro na ‘Continental Ebent Center’ da ke Katsina a ranakun Litinin da Talata, inda masana da kwararru suka tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci a zamanance.

Da yake jawabin bude taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Radda ya bayyana cewa taron zai maida hankali wajen noma da gine-gine da makamashi da fasaha da kuma ci gaba Dan’adam.

Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan taro na zama babban mataki wajen sauya fasalin tattalin arzikin Katsina. Ya jaddada cewa jihar ba kawai masu zuba jari take nema ba, har da abokan hulda na dindindin don samun ci gaba mai dorewa.

Radda ya yi ikirarin cewa Jihar Katsina tana da manyan filayen noma masu yalwa da yawan matasa masu kuzarin san aiki wadanda za su mayar da jihar wata mahada ta noma da manyan masana’antun sarrafa kayan amfani gona a nan gaba.

Ya bayyana shirin gwamnatinsa na mayar da Katsina cibiyar sufuri da jigilar kaya ta hanyar inganta hanyoyin mota, layin dogo da gine-ginen kan iyaka domin kara hadin Nijeriya da kasashen yammacin Afirka.

A fannin makamashi kuwa, Gwamna Radda ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na habaka makamashi ta hanyar sabunta hasken rana, iska da sauran sinadarai domin samar da ingantac-ciyar wutar lantarki ga gidaje da masana’antu a fadin Jihar Katsina.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa sabbin binciken kasa sun tabbatar da cewa Katsina na dauke da daya daga cikin manyan ma’adinan zinare masu daraja a Nijeriya, lamarin da ya ce hujja ce ta babbar damar arzikin jihar da ba a taba amfani da ita yadda ya kamata ba.

Tun da farko da yake jawabi, Darakta Janar na hukumar zuba hannu jari da bunkasa tattalin ar-ziki ta KIPA, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana taron a matsayin wani lokaci mai mu-himmanci da Jihar Katsina za ta yi alfahari da shi.

Alhaji Ibrahim ya kara da cewa Jihar Katsina za ta samu sauyi a fannin ci gaba da dogaro da kai ga kamfanoni da masu zuba hannu jari da zai dauki dogon lokaci ana cin moriyarsa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *