Hamɓararren Shugaban Guinea-Bissau ya gudu Senegal
[ad_1]
Hamɓararren Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya isa ƙasar Senegal bayan da sojoji da suka kifar da gwamnatinsa a wannan makon suka sake shi.
Wannan ya biyo bayan tattaunawar ƙungiyar ECOWAS yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a ƙasar sakamakon juyin mulkin.
Ma’aikatar harkokin wajen Senegal a cikin wata sanarwa ta ce Embaló ya sauka a cikin ƙasar “lafiya kalau” a jirgin sojoji da aka ɗauka a haya da yammacin Alhamis.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link