Tawagar Atiku Ta Isa Bauchi Don Halartar Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
[ad_1]
Tawagar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ta iso Bauchi da misalin ƙarfe 11:08 na safiyar yau Juma’a domin halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Shigowar tawagar ta jawo taruwar jama’a a filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa domin tarɓarsu.
An shirya gudanar da jana’izar Sheikh Dahiru da ƙarfe uku na rana a babban filin Idi da ke Bauchi, inda ake sa ran dubban mabiya Ɗarikar Tijjaniyya da sauran al’umma za su hallarci taron. Sheikh Dahiru Bauchi ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai masu tasiri a Nijeriya da yankin Afirka ta Yamma.
Daga cikin tawagar Atiku akwai tsohon shugaban rundunar Sojin sama, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, da wasu fitattun mutane daga fannonin siyasa da addini.
Mataimakin gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, tare da ƴaƴan Sheikh Dahiru, musamman waɗanda ke jagorantar Ɗarikar Tijjaniyya, su ne suka tarɓi tawagar a filin jirgin.
[ad_2]
Source link